Isa ga babban shafi
Liberia-Najeriya

Ebola: Liberia ta kafa dokar hana fitar dare

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta kafa dokar hana fita da dare a ci gaba da daukar matakan dakile bazuwar cutar Ebola da ta hallaka mutane da dama a kasar. Dokar zata fara aiki daga ranar Laraba 20 ga watan Agusta da misalin karfe 9:00 na dare zuwa 6 na safe.

Jami'an kiwon lafiya da ke  yaki da cutar Ebola a Liberia
Jami'an kiwon lafiya da ke yaki da cutar Ebola a Liberia REUTERS
Talla

Daukar wannan matakin kuma na zuwa ne bayan hukumomin Liberia sun ce an gano mutanen nan 17 da suka tsere daga inda ake kula da masu fama da cutar Ebola bayan wasu Matasa dauke da kulakai suka kai hari asibitin da ake kula da su tare da farfasa sansanin.

Ministan yada labaran kasar Lewis Brown yace an gano mutanen ne a wata cibiyar kula da lafiya kuma yanzu haka an killace su don ganin ba su yada cutar ba.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin duniya tace cutar ta kashe mutane 84 a cikin kwanaki uku, abin da ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola zuwa 1,229.

A kasar Liberia mutane 466 suka mutu daga cikin mutane 834 da suka kamu da cutar a kasar.

Cutar Ebola kuma ta kashe mutane kusan 400 a kasashen Guinea da Saliyo, yayin da mahukuntan Najeriya suka tabbatar da mutuwar mutum na biyar.

Mahukuntan Najeriya sun ce Dr Stella Adedavoh daya daga cikin likitocin da suka duba Patrick Sawyer dan Liberia da ya kai cutar zuwa cikin kasar, ta rasu jiya bayan kamuwa da cutar.

Kasar Saliyo ta yi bayanin cewar cutar ebola ta tsallaka cikin kasar ne sakamakon ikrarin da wata mai maganin gargajiya ta yi cewar tana da maganin cutar.

Mohammed Vandi, wani babban jami’in lafiyar kasar, yace matar da ke zama a wani kauye kusa da iyakar Guinea ta kamu da cutar lokacin da take kula da majinyata inda ta mutu.

Vandi yace mutanen da suka halarci jana’izarta a lokacin ne suka kamu da cutar inda suka yada ta har aka samu mutane 365 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.