Ma'aikatan sa-kai 800 don hana yaduwar Ebola a Lagos
Gwamnatin jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya, ta ce yanzu haka ta horas da masu aikin sa-kai akalla 800 domin taimaka wa sauran jami’an kiwon lafiya da ke yaki da cutar Ebola da kawo yanzu ta kashe mutane 4 a birnin.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun gwamnan jihar Lagos Babatunde Raji Fashola, wato Mista Hakeem Bello, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, yanzu haka an rarraba wadannan ma’aikatan sa-aka zuwa wasu unguwanni 57, to sai dai ya ce har yanzu akwai bukatar karin jama’a a wannan aiki.
Kawo yanzu dai cutar ta Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 1,145 a kasashe 4 na yammacin Afirka ciki har da Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu