Isa ga babban shafi
Mozambique

Jagoran ‘Yan tawayen Mozambique ya koma Maputo

Jagoran ‘yan tawayen kasar Mozambique Afonso Dhlakama ya fito a bainar jama’a a Mozambique bayan da ya dade yana buya, inda aka ce yanzu ya koma a birnin Maputo, a wani mataki da ake ganin zai kawo karshen tashin hankalin siyasa na shekaru biyu a kasar.

Afonso Dhlakama, Shugaban Renamo, a Mozambique
Afonso Dhlakama, Shugaban Renamo, a Mozambique AFP PHOTO / JINTY JACKSON
Talla

Rahotanni sun ce dandazon magoya bayan Afonso Dhlakama ne suka kwashe sa’o’i suna jira a filin jirgin kasar da ke a Maputo kafin isowarsa.

Tun a Watan Okotoban shekarar 2012 ne Dhlakama ya yi layar zana ba’a sake ganin shi ba inda ya koma a tsakiyar Mozambique yana kuma kalubalantar gwamnatin kasar akan rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 1992.

Yarjejeniyar dai ta kare ne bayan shekaru 15 ana tafka kazamin yakin basasa da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane miliyan guda.

Yakin ne dai ya zabtare jagorancin gwamnatin hadin guiwa ta jam’iyyun Mozambican National Resistance, da jam’iyyar Marxist Mozambique Liberation Front ta farko a karkashin Dhlakama da ya karbi mulki bayan samun ‘yancin kan kasar daga kasar Portugal a shekarar 1975.

A shekarar 2013 ne dai jagoran na jam’iyyar RENAMO ya shiga buya a yankin tsaunukan Gorongosa.

Dattijon mai shekaru 61 dai ya yi tsayawa takara a dukkanin takarar shugaban kasar da aka shirya tun daga 1994, amma goyon bayansa ya ragu zuwa kashi 16 a zaben shekarar 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.