Isa ga babban shafi
Najeriya

Ebola: Ana kula da yanayin lafiyar mutane 160 a Fatakwal

Mahukuntan lafiya a Najeriya sun ce suna kula da yanayin lafiyar mutane 160 bayan bullar cutar Ebola a garin Fatakwal a Jihar Rivers da ke kudancin kasar inda aka samu mutuwar wani likita sakamakon kamuwa da cutar. Kwamishinan lafiya na Jihar yace zuwa yanzu cikin mutanen 160 babu wanda ya nuna alamun yana dauke da Ebola, amma suna ci gaba da tuntubarsu domin sanin yanayin da suke ci.

Likitocin Ebola a Liberia
Likitocin Ebola a Liberia REUTERS/2Tango
Talla

A ranar Alhamis ne dai aka tabbatar da mutuwar wani Likita a garin Fatakwal, mutum na farko da ya kamu da Ebola a wani gari sabanin Lagos inda mutumin Liberia ya fara kawo cutar a Najeriya.

Sai dai duk da wannan barazana ta Ebola a garin na Fatakwal amma kungiyar da ke yakin neman zaben shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wa’adi na biyu tana can tana gudanar da taronta kamar yadda ta shirya a yau Assabar. Kuma zuwa yanzu babu wani gargadi daga mahukuntan Lafiya a Najeriya game da taron don kaucewa bazuwar cutar Ebola da ke yin kisa cin hanzari.

Mutane 6 suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Ebola. Yayin da cutar ta kashe mutane sama da 1,500 a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.