Isa ga babban shafi
Najeriya

Ebola: Wani Likita ya mutu a Fatakwal

Ministan Lafiya a Najeriya Onyebuchi Chukwu ya tabbatar da mutuwar wani Likita a garin Fatakwal da ke kudu maso gabacin kasar, sakamakom kamuwa da cutar Ebola, wanda shi ne karon farko da aka samu bullar cutar a wani gari sabanin Lagos.

Jami'an Kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a birnin Monrovia, na Libéria.
Jami'an Kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a birnin Monrovia, na Libéria. REUTERS/2Tango
Talla

Ministan yace likitan ya mutu ne a ranar 22 ga watan Agusta bayan kula da lafiyar daya daga cikin mutanen da suka yi mu’amula da mutumin kasar Liberia da ya shigo da cutar a a garin Lagos a ranar 25 ga watan Yuli.

Ministan yace sun samu labarin mutuwar Likitan ne daga matarsa, kuma binciken da suka gudanar ya tabbatar da cewa Likitan ya mutu ne sakamakon kamuwa da cutar Ebola.

Yanzu mutane shida ken an suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Ebola. A cikin makon nan ne Ma'aikatar Lafiya a Najeriya tace mutum guda ne yanzu ya rage da aka killace ana kula da lafiyarsa bayan sallamar wasu  da dama da suka yi mu'amula da Patrick Sawyer mutumin Liberia da ya kawo cutar a Najeriya.

Mutane 1,428 suka mutu daga cutar Ebola a bana, yawancinsu a kasashen Saliyo da Laberiya da Guinea, kuma zuwa yanzu mutane 2,615 ke dauke da cutar a kasashen.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da Ministocin Lafiya a kasashen yammacin Afrika ke tattauna batun barazanar cutar Ebola a yankin a birnin Accra na kasar Ghana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.