Isa ga babban shafi
Liberia

Ebola: An rufe Makarantu a Liberia

Shugabar Kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta bukaci rufe daukacin makarantun kasar da kuma bai wa ma’aikatan gwamnati wadanda ayyukan su bai zama wajibi hutun wata guda a wani mataki na dakile yaduwar cutar Ebola a kasar.

Shugabar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf tana magana da RFI
Shugabar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf tana magana da RFI DR
Talla

A jawabin da ta yi wa al’ummar kasar a talabijin, shugaba Sirleaf tace daukar matakin ya biyo bayan shawara da ma’aikatar ilimi ta bayar domin kare dalibai.

Liberia na daya daga cikin kasashen da cutar Ebola ta yi wa illa inda aka samu mutuwar mutane 129 cikin mutane 249 da suka kamu da cutar.

Tuni mahukuntan Liberia suka haramta gudanar da kwallon kafa a cikin kasar domin dakile yaduwar cutar Ebola.

Zuwa yanzu cutar Ebola ta kashe Mutane 672 cikin mutane 1,200 da suka kamu da cutar a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.