Likitan Amurka ya kamu da Ebola a Liberia
Wani likitan kasar Amurka da ke aikin kula da cutar Ebola, shi ma ya kamu da cutar a kasar Liberia. Wata Kungiyar agaji tace an kwantar da Likitan mai suna Dr Kenta Brantly a wata Asibiti a birnin Manrovia a kasar Liberia.
Wallafawa ranar:
Likitan yana aiki ne da wata Kungiyar agaji ta Samaritan Purse, kuma a cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na Intanet, tace Likitan yana da Mata da ‘yaya biyu.
Cutar Ebola dai yanzu ta zama annoba a yammacin Afrika inda a kwanan ne aka samu bullar cutar a Najeriya bayan ta yi kisa a kasashen guine da Liberia da Saliyo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu