Isa ga babban shafi
Najeriya

Cutar Ebola; Tawagar ma'aikatar lafiya ta kasa ta isa Lagos

Bayan da wani dan kasar Liberia ya mutu sakamakon cutar Ebola a birnin Lagos da ke kudancin Nigeria, hukumomin kasar suka fara daukar matakan ganin cutar ba ta ci gaba da yaduwa zuwa sauran yankunan kasar ba.

Dr Jide Idris, kwamishin lafiya na jihar Lagos a Najeriya
Dr Jide Idris, kwamishin lafiya na jihar Lagos a Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Yanzu haka dai wata tawaga da ta kunshi kwararri kan sha’anin kiwon lafiya ta tarayyar kasar ta isa a birnin Lagos domin samar da dubarun hana yaduwar cutar da kuma tantance wadanda suka yi mu’amala da dan kasar Liberia da ya rasu sabado da cutar.

Dr Nasiru Sani Gwarzo na maikatar lafiyar kasar, sannan daya daga cikin tawagar da suka isa birnin Lagos don wannan aikin, ya kuma shaida wa Sashen Hausa na rediyo Faransa RFI cewa tuni suka tantance mutane da dama da suka yi mu’amalar da marigayin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.