Isa ga babban shafi
AU

Kungiyar Amnesty ta yi Allah wadai da shugabannin Afrika

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amesty, ta yi Allah wadai da matakin da kungiyar hadin kan kasashen Africa ta AU ta dauka, na bayar da kariya daga gurfana a gaban kotu, ga shugabannin Afrika da ake zargi da aikata manyan laifuka.

Sakatare Janar na Amnesty International, Salil Shetty a lokacin gabatar da wani rahoto
Sakatare Janar na Amnesty International, Salil Shetty a lokacin gabatar da wani rahoto REUTERS/Mohammed Dabbous
Talla

Kungiyar ta bayyana takaicin daukan wannan matakin ne, cikin rahoton da ta fitar a jiya talata.

Cikin rahoton, kungiyar ta Amnesty ta bayyana matakin da kungiyar ta AU ta dauka, na hana gurfanar da shugabannin kasar da ake zargi da kisan kare dangi, aikata laifukan yaki da cin zarafin bil Adama, da cewa koma baya ne.

Yayin taron da suka yi a ranakun 26 da 27 na watan Yunin daya gabata a kasar Equatorial Guinea, Shugabannin sun kada kuri’ar amincewa da kudurin.

Shi dai wannan kudiri, daya hana gurfanar da shugabannin kasashen Afrika da ma manyan jami’an gwamnati a gaban kotun hukunta manyan laifuka da kare hakkin dan Adam da ake shirin kafawa.

Darakta mai kula da harkokin nahiyar Africa a kungiyar ta Amnesty Netsanet Belay, ya ce ba yadda za a amince da wannan matakin ba, a lokacin da nahiyar ta Afrika ke kokarin tabbatar da mulki na gari.

Sai dai duk da wannan matakin da shugabannin na Afrika suka dauka, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na da damar bincikar shugabannin, kan wadannan laifukan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.