Isa ga babban shafi
Chadi-Afrika ta Tsakiya

Rufe iyakan Chadi da Afrika ta tsakiya matsala ne-Amnesty

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International, tace matakin da kasar Chadi ta dauka na rufe iyakarta da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zai katse kai dauki ga dubban Yan gudun hijirar da ke kasar.

Sansanin 'Yan gudun hijira da ke ficewa Bangui kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika
Sansanin 'Yan gudun hijira da ke ficewa Bangui kasar Jamhuriyyar tsakiyar Afrika © EU/ECHO/Patrick Lambrechts
Talla

Sanarwar da kungiyar ta bayar mai dauke da sanya hannu Christian Mukosa, Daraktan bincikenta a Yankin Afrika ta Tsakiya, ya bukaci hukumomin Chadi su sauya matsayin su wajen bude iyakar kasar.

Kungiyar ta kuma bukaci kasashen duniya su gaggauta wajen kai wa dubban 'yan gudun hijirar da suka gujewa wanna tashin hankali mai nasaba da kabilanci da addini dauki wajen tallafa musu abinda zasu ci da matsuguni.

Mukosa yace yanzu haka mutane sama da 360,000 suka gudu daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya domin tsira da rayukansu, sakamakon tabarbarewar al'amura da ya kai ga kisan kiyashi.

Kungiyar tayi gargadi kan mayar da yan gudun hijira cikin Afrika ta Tsakiya inda ta ke cewar yin haka zai jefa rayuwarsu cikin mummunan hadari, ganin yadda har yanzu ana samun 'yan gudun hijirar da ke tafiya a kasa na watanni biyu daga Bangui zuwa Chadi.

Iyakar Chadi da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dai na da nisan kilomita sama da 1,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.