Isa ga babban shafi
Najeriya

Sabon rikici ya barke tsakanin makiyaya da manoma a Benue

Sabon tashin hankalin ya barke tsakanin Fulani makiyaya da Manoma a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya inda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 7.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Talla

Ko a cikin makon da ya gabata an samu barkewar irin wannan rikici wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13. Kakakin gwamnatin jihar Daniel Ezeala ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, makiyaya ne suka kai wa manoma harin.

Wasu rahotanni kuwa na cewa wasu mutane dauke da makamai sun kai wa ayarin matafiya ‘yan asalin jihar Sakkwato a lokacin da suka isa garin Boko na jihar ta Benue, inda suka kashe biyar daga cikin matafiyan sannan suka cinnawa motar da suke tafiya cikinta wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.