Isa ga babban shafi
Najeriya

An kai hare-hare bam a birnin Maiduguri

An kai hare-haren kunar bakin wake har guda a garin Maiduguri da ke jihar Borno a Tarayyar Najeriya a yau talata, inda aka aka tabbatar da mutuwar mutane akalla 11 cikinsu kuwa har da jami’an tsaro.

Hari kan gidan yarin Maiduguri
Hari kan gidan yarin Maiduguri (Photo : Reuters)
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Borno Gideon Jibrin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda da farko wata mota ce aka tarwatsa da misalin karfe 7 da rabi na safe agogon kasar, kuma an samu mutuwar mutune 3 nan take, sai kuma hari na biyu wanda bam ne aka fasa akan motar ‘yan sanda minti 10 bayan faruwar harin na farko, kuma an samu asarar rayukan ‘yan sanda 5 a lokacin.

Wata majiya ta ce an kashe wasu mutane uku da ake zargin cewa dukkaninsu magoya bayan kungiyar Boko Haram ne a garin na Maiduguri a yau talata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.