Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi; Muhimmancin harshen uwa ga ci gaban kimiya

Wallafawa ranar:

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tabo bayani ne akan Harshen uwa ta lakari da ilimin harshen hausa da muhimmancinsa ga ci gaban kimiya da fasaha. A ranar 21 ga watan Fabrairu ne hukumar Ilimi da bunkasa al’adu ta UNESCO ta ware domin inganta harsunan uwa tsakanin al’ummar kasashen duniya.

Ranar Harshen uwa ta duniya
Ranar Harshen uwa ta duniya DR
Talla

Taken bikin ranar harshen uwa a bana shi ne irin rawar da harshe ke takawa ga ci gaban kimiya.

A cikin jawabin sakonsa a ranar bikin harshen uwa a bana, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya danganta sakonsa da kalaman marigayi Nelson Mandela tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu, wanda yace idan har ka yi Magana da mutum da harhsen da ya ke ji to sakonka zai tsaya ne a kansa amma idan da harshen uwa ne sakon zai kai ga zuciyarsa. Wanda wannan ke nuna muhimmacin harshen uwa.

Domin inganta harshen Hausa, a Jamhuriyyar Nijar an gudanar da taro na hadin gwiwa tsakanin kungiyar marubuta da manazarta na Nijar da kungiyar manazarta harsunan gida na Najeriya na tsawon kwanaki uku a watan Fabrariu da aka yi bikin harshen uwa domin karrama Farfessa Hambali Junju wanda ya taka muhimmiyar rawa ga ci gaba da bunkasar harshen hausa musamman fassarar kalaman kimiya. Shirin Ilimi ya halarci zaman taron kamar yadda zaku ji  a cikin shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.