Isa ga babban shafi
Masar

Morsi ya ce har yanzu shi ne Shugaban Masar

Hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya yi watsi da zarge zargen da ake masa a lokacin da ya gurfana a gaban kotu a yau Litinin tare da kira ga Kotun ta hukunta shugabannin gwamnatin Sojojin da suka hambarar da gwamnatin shi.

Wasu magoya bayan Hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi zuna zanga-zanga a birnin Al kahira
Wasu magoya bayan Hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi zuna zanga-zanga a birnin Al kahira ©Reuters.
Talla

Dubban magoya bayan Morsi ne suka fito suna gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansa wanda shi ne shugaban Dimokuradiya na farko a kasar Masar.

Hambararren shugaban na ya bayyana ne a gaban Kotun  da ke birnin Al Qahira domin amsa tuhumar da ake yi masa na mutuwar wasu masu zanga zanga a rikicin siyasar da ya kunno kai a zamanin mulkinsa.

Babbar Kotun kasar ta dage sauraren karar zuwa ranar 8 ga watan Janairu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ruwaito cewa an kai Morsi kotun ne a wani jirgi mai tashin angulu tare da wasu mutane 14 da ake tuhumarsu tare.

Tun a ranar uku ga watan Yuli ne aka hambarar da gwamnatin Morsi, lamarin da ya sa ba a ji duriyarsa ba tun daga lokacin.

Rahotanni sun ce sojin kasar sun rike shi ne a wani wuri da ba a bayyana ba.

Tuni hukumomin kasar suka sa ‘Yan sanda 20,000 domin aikin ko ta kwana saboda rikicin da ake gudun kada ya barke yayin da aka saka shinge mai fadi a harabar kotun domin tsare magoya bayan Morsi.

Wannan shari’a za ta nuna irin kamun ludayin sabbin hukumomin kasar ta Masar wadanda kungiyoyin fararen hula suke suka da yin amfani da karfi mai tsanani wajen gudanar da ayyukansu.

Tuni kungiyar Kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi kira da a yi adalci a shari’ar musamman wajen tabbatar an ba Morsi damar ya kare kanshi daga zargin da ake yi mai.

“Ya kamata a yi mai adalci a shari’ar, a kuma ba shi dama ya kare kanshi daga zargin da ake masa.” Inji kungiyar.

Kakakin Ma’aikatar shari’ar kasar Badr Abdelatty ya gayawa manema labarai cewa za 'a tuhumi Morsi ne bisa tsarin yadda doka ta tsara.

“Babu wani banbanci, babu wariya, za a  tabbatar da adalci”, inji Abdelatty.

A daya bangaren kuma a jiya Lahadi ne Sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya kai wata ziyarar aiki a kasar Masar inda ya bayyana aniyar Amurka na yin aiki kafada da kafada da hukumomin kasar.

Sai dai Kerry ya yi kira ga hukumomin Masar da su yi kokari su mayar da kasar bisa turbar demokuradiyya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.