Isa ga babban shafi
Masar

An cafke wani babban shugaban ‘yan uwa musulmi a Masar

Hukumomi a Masar sun sanar da cafke Essam al – Erian, daya daga cikin manyan shugabannin ‘yan uwa musulmi, wanda yana daya daga cikin kalilan da na kungiyar dab a a kama ba.

Hanun wani masoyin Morsi a kusa da hotanshi
Hanun wani masoyin Morsi a kusa da hotanshi AFP PHOTO/OZAN KOSE
Talla

Rahotanni sun ce da sanyin safiyar yau Laraba aka kama Erian a birnin Alqahira wanda shine mataimakin shugaban jam’iyar Freedom and Justice Party.

Hotunan bidiyo da aka watsa kafofin sada zumunta sun nuna Erian yana murumushi yayin da aka kama shi, yana kuma mai nuna alamar adawa da hambarar da gwamnatin Shugaba Mohammed Morsi.

Tun a watan Agustan wannan shekara sojin kasar suka fara farautar magoya bayan Morsi lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a lokacin da sojin suka tarwtsa wani sasanin masu adawa da sauyin gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.