Isa ga babban shafi
Somalia

Gwamnatin Somalia ta sasanta da shugaban Jubaland

Gwamnatin Somalia ta kulla yarjejeniyar amincewa da wani tsohon kwamnadan ‘Yan tawaye domin ya zama shugaban rikon kwarya na yankin Juba da ke kudancin kasar. A cewar majiyoyin gwamnati, amincewa da hakan zai taimaka wajen kawo karshen fadan da ake fafatawa tsakanin magoya bayansa da kuma dakarun gwamnati.

Sheikh Ahmed Madobe, wanda ya jima yana gwagwarmaya domin kafa kasar Jubaland a yankin Kismayo da ke gabar ruwan Somalia
Sheikh Ahmed Madobe, wanda ya jima yana gwagwarmaya domin kafa kasar Jubaland a yankin Kismayo da ke gabar ruwan Somalia
Talla

Yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin bangarorin biyu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha bayan share tsawon kwanaki ana tattaunawa, wani muhimmin ci gaba ne wajen samar da zaman lafiya a kasar a cewar wata majiyar gwamnatin kasar ta Somalia.

Wani wakilin gwamnatin Magadishiu ne ya sanya hannu akan wannan yarjejeniya da shugaban ‘yan tawayen mai suna Sheik Ahmad Madobe, wanda ya jima yana gwagwarmaya domin kafa kasar Jubaland a yankin Kismayo da ke gabar ruwan kasar.

Samar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu zai taimaka wajen ciyar da tattalin arzikin kasar Somalia musamman ma ta la’akari da cewa yankin na a matsayin wanda ke da dimbin arziki, da tashar jiragen ruwa da kuma ruwan tekun da ake kamun kifi a cikinsa.

Minista na musamman a fadar shugaban kasar mai suna Farah sheik Abdulkadir, wanda ke zantawa da manema labarai dangane da wannan sulhu, ya ce hakan na a matsayin wata dama ta kara fadada karfin ikon gwamnati zuwa sauran yankunan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.