Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

Ana shirin yin zaben 'yan majalisa a Guinea Conakry

An kaddamar da yakin neman zaben ‘yan Majalisar dokoki a kasar Guinee Conakry, wato kusan shekaru uku kenan da zaben shugaban kasar amma ba Majalisa.Wannan na zuwa ne yayin da ake fargabar yiyuwar samun tashe-tashen hankula a wannan lokaci, musamman ma ganin cewa ko a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata an samu barkewar rikicin kabilanci da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 50 a kudancin kasar.Hukumomin tsaro na ci gaba da farautar wasu fursunoni da suka tsere daga gidan yarin wani gari mai suna Mamou a gabashin birnin Conakry na kasar ta Guinee ajiya lahadi.Rahotanni sun ce akalla fursunoni 30 ne, cikinsu kuwa har da wadanda suka aikata miyagun laifuka, suka tsere.To sai dai wasu bayanai na cewa an samu nasarar cafke wasu daga cikin gudaddun, sakamakon gudunmuwar da jama’ar garin suka bayar wajen kame su. 

Shugaban kasar Guinee Conakry, Alpha Condé
Shugaban kasar Guinee Conakry, Alpha Condé AFP/ CELLOU BINANI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.