Isa ga babban shafi
Mali

Mali: Boubacar Keita ya sha alwashin sake hada kan ‘yan kasar

Zababben Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita, ya dauki aniyar sake hada kan ‘Yan kasar, daga matsalar siyasa, juyin mulki da kuma yakin da ya rarraba kawunansu.

Zababben shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keïta
Zababben shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keïta REUTERS/Joe Penney
Talla

Duk da yake ana cigaba da dakon sakamakon zabe daga hukumomin kasar, tuni Soumaila Cisse, ya amsa shan kaye, kuma ya yi tattaki zuwa gidan Keita inda ya taya shi murna.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya bayyana farin cikinshi da zaben, inda ya sanar da aniyar sa na halartar bikin rantsar da sabon shugaban.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka sake gudanar da zabe a zagaye na biyu bayan ‘yan takarar sun gaza samun kuri’u masu rinjaye.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.