Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Shugaba Hollande zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban Mali

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce zai halarci bikin rantsar da Ibrahim Boubakar Keita a matsayin sabon shugaban kasar Mali bayan nasarar da ya sama a zaben shugabancin kasar na ranar lahadin da ta gabata.

Ibrahim Boubacar Keïta, yana jefa kuri'a ranar 11 ga watan Agusta 2013.
Ibrahim Boubacar Keïta, yana jefa kuri'a ranar 11 ga watan Agusta 2013. REUTERS/Joe Penney
Talla

Wata sanarwa da fadar shugaban na Faransa ta fitar, ta ce a yau da safe, Hollande ya kira zababben shugaban na Mali ta wayar tarho domin taya shi murnar nasarar da ya sama, inda kuma ya yi alkawalin cewa Faransa za ta ci gaba da taimakawa Mali domin dawo da kasar akan turbar zaman lafiya bayan wannan zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.