Isa ga babban shafi
Najeriya

An bude taron kasashen Afrika a Abuja

An bude babban taron shugabanin kungiyar kasashen Nahiyar Afrika na musamman a Abuja babban birnin Najeriya inda Shugabanin kasashen za su yi nazari kan ci gaban da ake samu wajen yaki da cutar kanjamau da cizon sauro da kuma tarin fuka.

Taron shugabannin kasashen Nahiyar Afruka
Taron shugabannin kasashen Nahiyar Afruka
Talla

Gabanin taron dai Kungiyoyin fararen Hula na Nahiyar Afrika daga kasashe daban-daban, sun bukaci hana shugaban kasar Sudan, Omar Hassan al-Bashir halartar taron, saboda abinda suka kira sammacin kotun hukunta manyan laifufuka da ke a gabansa.

Mun yi iya bakin kokarin mu dan jin ta bakin Ministan harkokin waje a tarayyar Najeriya, Dr Nurudeen Muhammed domin jin karin bayani kan wannan batu, amma bai dauki waya.

Najeriya dai ta kasance Mamba a babbar Kotun hukunta masu manyan laifuka ta Duniya wato ICC wadda ta caji shugaba Omar al-Bashir da aikata laifukan yaki da zub da Jini kazalika da cin zarafin bil’adama a kasar Sudan.

Ofishin jakadancin kasar Sudan a Najerya dai ya bayyana cewar tabbas shugaba al-Bashir zai halarci taron da za’a gudanar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.