An nada shugaban rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Mali
Babban Magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya nada Bert Koenders dan kasar Holland a matsayin shugaban rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar a kasar Mali.
Wallafawa ranar:
Ita dai wannan runduna wadda za to soma aiki a ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara, babban aikin da ya rataya a wuyanta shi ne kokarin dawo da tsaro a kasar mai fama da yakin basasa, sannan kuma za ta taka rawa domin samar da yanayin shiga tattaunawa tsakanin gamnati da kuma ‘yan tawayen kungiyar MNLA.
A can baya dai, Bert Koenders, ya taba rike mumakin shugaban rundunar MDD a kasar Cote d’Ivoire wato ONUCI, kuma rundunar da zai jagoranta a kasar ta Mali, za ta kunshi dakaru akalla dubu 12.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu