Isa ga babban shafi
Libya

An kai harin bam a birnin Benghazi da ke gabashin Libya

Wani harin bam da ya faru a sanyin safiyar yau asabar a birnin Benghazi da ke gabashin kasar Libya ya haddasa mummunar barna ga wani gini, duk da cewa ba a samu asarar rayukan jama’a ba.

Hari kan ofishin jikadancin Amurka a Benghazi
Hari kan ofishin jikadancin Amurka a Benghazi REUTERS/Esam Al-Fetori/Files
Talla

Babban jami’in ‘yan sanda a yankin da lamarin ya faru mai suna Kanar Matar Mohammed, ya ce bam din ya fashe ne da misalin karfe 6 na safe agogon kasar, kuma yanzu haka suna kan gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu wajen tayar da shi.
Ko a ranar talatar da ta gabata an kai harin bam a kan ginin ofishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Tripoli inda ya raunata mutane da dama. A can kuwa birnin Benghazi, ko a cikin makon da ya gabata wasu dauke da makamai sun kai hari a kan wani ofishin ‘yan sanda inda suka ‘yantar da mutane da dama da ke tsare a wurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.