Isa ga babban shafi
Mali

Karfin ikon Mali: Sojoji a Kati ko farar hula a Bamako?

Sabon Firaministan kasar Mali Diango Cissoko ya yi alkwalin kafa gwamnatin Hadaka a lokacin da zai fara tafiyar da ayyukan kasar. Amma yanzu ana ganin karfin fada aji ya koma barikin Soji a Kati maimakon birnin Bamako bayan tube Cheick Modibo Diarra a matsayin Firaminista.

Shugaban Mali Diouncounda Traore tare da  Amadou Haya Sanogo bayan sun gana a Hedikwatar Soji da ke Kati
Shugaban Mali Diouncounda Traore tare da Amadou Haya Sanogo bayan sun gana a Hedikwatar Soji da ke Kati Reuters/Joe Penney
Talla

Wakilin RFI a Mali yace birnin Kati birni ne na Sojoji inda yana da wahala a samu gida a garin a rasa samun Soja ko Dan Sanda.

Wani mazauni garin Kati yace suna alfahari da yanayin garin mai cike da sojoji kuma sun ji dadin yadda Amadou Sanago ya jagoranci juyin mulkin da suka yi wa gwamnatin Farar hula ta Amadou Toumani Toure.

Tun bayan hambarar da Gwamnatin Farar hula, Amadou Sanogo ke ci gaba da bayar da umurnin tafiyar da mulkin kasar Mali daga birnin Kati.

A kasar Mali wasu sun fara hasashen cewa Sanogo zai tube kaki ya tsaya takarar shugabancin kasar a zabe.

Wani al’amari da ya tabbatar da karfin Sanogo shi ne bayar da umurnin tube Firaminista daga madafan iko.

Kaftin Sanogo dai shi ne shugaban kwamitin rundunar tsaro a kasar Mali wanda ke da ikon karkatar da jami’an tsaron kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.