Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

‘Yan Tawayen Congo sun karbe ikon birnin Goma

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da matakin kakabawa wasu daga cikin shugabanin ‘Yan Tawayen Janhuriyar Demokradiyar Congo Takunkumi, wannan kuma na zuwa ne bayan ‘Yan tawayen sun karbe ikon garin Goma.

Tawagar rundunar 'Yan tawayen Congo a a cikin garin Goma
Tawagar rundunar 'Yan tawayen Congo a a cikin garin Goma REUTERS/James Akena
Talla

Tuni dai ‘Yan Tawayen na Congo suka fara karbe ikon Filin saukar Jirgin Birnin Goma kafin su kutsa kai cikin birnin da ke gabacin kasar. Kungiyar Tarayyar Afrika ta yi Allah Waddai da hare haren da Kungiyar ke kai wa.

Akwai dubban mutane da suka gudu zuwa birnin Goma domin kauracewa rikicin ‘Yan tawayen.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa game da rikicin na ‘Yan tawaye.

Sai dai kuma Majalisar ta zargi kasashen Rwanda da Uganda da ke makwabtaka da Jamhuriyyar Congo a matsayin kasashen da ke taimakawa ‘Yan tawayen. Zargin da kasashen biyu suka yi watsi da shi.

‘Yan tawayen sun sake kaddamar da rikicin ne a makon jiya bayan Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun kakabawa shugabansu Takunkumi.

‘Yan tawayen na M23 sun ce suna yaki ne domin karya gwamnatin Jamhuriyyar Congo.

Akwai dai dakarun Majalisar Dinkin Duniya 1,500 da aka girke domin yaki da ‘Yan tawayen.

'Yan tawayen M23, tsoffin Sojojin Jamhuriyyar Congo ne da suka rikide suka koma ‘Yan tawaye

Tun shekarar 1998 an ruwaito sama da mutane Miliyan Uku suka mutu sanadiyar Rikicin kasar, wasu Miliyan Daya da Dubu Dari Shida kuma sun mutu ne saboda cutuka da rashin abinci.

Shugabar kungiyar ta taraiyyar Africa Nkosazana Dlamini-Zuma, ta yi kiran a kai dauki ga wadanda Rikicin ya rutsa da su, wadanda yawancin su fararen hula ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.