Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta zargi jami’an tsaron Najeriya da cin zarafin Al’umma

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International, ta zargi jami’an tsaron Najeriya da wuce gona da iri wajen yakin da suka kaddamar don farautar ‘Yan kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Liadda’awati wal Jihad da ake kira da sunan Boko Hraam.

Jami'an tsaron Najeriya suna sintiri a saman titi bayan saka dokar hana Fita a cikin biranen Arewacin kasar
Jami'an tsaron Najeriya suna sintiri a saman titi bayan saka dokar hana Fita a cikin biranen Arewacin kasar sphotos-a.xx.fbcdn.net
Talla

Wani rahotan da kungiyar ta fitar, ya zargi jami’an tsaron da azabtar da mutane da kuma kashe wasu da ba su ji ba su gani ba. Kungiyar tace, yadda jami’an tsaron ke gudanar da ayyukansu kan haifar da tashin hankali a cikin kasar, abinda kuma ya tilasatawa daruruwan mutane tserewa daga gidajensu don tsira da ransu.

Dakta Hussein Abdu na kungiyar Action Aid, yace al’ummar Najeriya suna cikin tsaka mai wuya saboda hare hare daga ‘Yan Bindiga da kuma Jami’an tsaro.

Kungiyar Amnesty ta yi kira ga Gwamnatin Najeriya  domin daukar matakan gano laifin da ya shafi Boko Haram da kuma laifukan da Jami’an tsaro suka aikata don hukunta masu laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.