Isa ga babban shafi
Rwanda

Kotu ta yankewa wani hafsan sojin Rwanda hukuncin shekaru 9

Wata kotun soja a kasar Rwanda ta yankewa Laftanar Kanar Rugigana Ngabo hukuncin zaman gidan yari na shekaru tara.Ngabo tare da lauyansa sun ce za su daukaka kara akan wannan hukunci. 

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame
Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame Reuters
Talla

Ngabo, dan uwan babban sojan nan ne Faustin Kayumba Nyamwasa wanda ya nemi mafaka a kasar afrika ta kudu.

Ana zargin Ngabo da yin barazana ga tsaron kasa inda aka kamashi a watan Agustan 2010.

A watan Yunin 2010, an taba kai wa dan uwan Ngabo, Nyamwasa harin kisa inda ya zargi gwamnatin Shugaba Paul Kagame.

Amma gwamnatin ta Rwanda ta dade ta na musanta hakan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.