Isa ga babban shafi
DRC Congo, Rwanda

Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da Rwanda sun amince da dakile ayyukan ‘Yan tawaye

Kasashen Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Rwanda, sun amince akai musu dakarun samar da zaman lafiya daga kungiyar kasashen Afrika, domin yaki da Yan Tawayen Janar Bosco Ntaganda.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame tare da takwaransa shugaban kasar  Congo Joseph Kabila
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame tare da takwaransa shugaban kasar Congo Joseph Kabila © France 24
Talla

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, ya bayyana haka, bayan ganawar da su ka yi ta farko da shugaba Joseph Kabila, tun bayan rahotan Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya zargi kasar da taimakawa Yan Tawayen.

Shugaban ya ce ya zuwa yanzu ba’ a amince da yawan dakarun ba, da kuma kasashen da za su fito, da kuma lokacin da za’a girke su.

Shawarar aika dakarun ta samo asali ne bayan taron da aka gudanar na ministocin harkokin wajen kasashen da ke yankin Great Lakes da aka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata.

‘Yan Tawayen kungiyar M23, wanda Bosco Ntaganda ke jagoranta a wannan wata sun saka dakarun kasar ta Congo sun arce a yayin da dubbanin fararen hula su ka fice daga gidajensu a loakcin da su ka matsa kusa da gabashin Congo.

Kasar ta Congo ta na zargin kasar ta Rwanda da bawa ‘yan tawayen na Congo makamai, zargin da gwamnatin ta Rwanda ta musanta.

Matsalar rashin tsaron da ke addabar gabashin Congon ya samo asali ne daga rikicin ‘yan kabilar Tusti da Hutu wanda yai sandiyar mutuwa da kuma ficewar fara hula sama da miliyan daga gidajensu a kasar Rwanda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.