Isa ga babban shafi
Ghana

Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills ya rasu

Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills ya rasu bayan wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya da ya yi. Fadar Shugaban kasar ta Ghana ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar. Sanarwar da fadar ta fitar ta nuna cewa rashin lafiyar da shugaban ya yi ‘yar gajeruwa ce inda ta kara da cewa ya rasu ne sa’oi kadan bayan an kai shi asibiti.  

Marigayi Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills
Marigayi Shugaban kasar Ghana, John Atta Mills REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Amma baya ga wannan sanarwar babu wani bayani da ya fito akan mutuwar ta shugaban.

Dan shekaru 68 a duniya, an haifi Atta Mills a ranar 21 ga watan Yuli a shekarar 1944 a kauyen Tarkwa, mai arzikin zinare da ke kasar ta Ghana.

Ya samu digirinsa na farko ne a fannin shara’a a Jami’ar Ghana kafin ya zama Dakta a fannin ilimin sanin kasashen yammaci da na Afrika a Jami’ar birnin Landon.

A shekarar 1988, aka nada John Atta-Mills inda ya rike mukamin komishinan Ma’aikatar Haraji ta kasar Ghana.

Memba a jam’iyar National Democratic Congress, (NDC) a ranar 7 ga watan Janairun 1997 Atta Mills ya zama mataimakin shugaban kasar Ghana, Jerry Rawlings. 

Mukamin da ya rike har ranar 7 Janairun 2001, sau biyu a gwamnatin tsohon shugaban kasa John Kufuor. 

Mills ya karbi ragamar shugabancin kasar ta Ghana a watan Janairun shekarar 2009 bayan ya lashe zaben da aka gudanar da kashi daya a shekarar 2008.

Kamin ya samu nasarar shugabantar kasar, sau biyu ya nemi kujerar bai samu ba.

A watan Yulin shekarar da ta gabata ne Jam’iyarsa ta tsai da shi a matsayin dankararta na zaben da za a gudanar a watan Disembar wanna shekara.

John Atta Mills ya rasu ya bar mata daya da da daya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.