Isa ga babban shafi
Najeriya

Ambaliya ta yi sanadiyar hasarar rayuka a garin Jos na Najeriya

Ruwan Sama da aka tabka a garin Jos a Najeriya ya haifar da ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 40 tare da raba mutane da gidajensu sama da 200.

Wani Yanki da Ambaliyar Ruwa ta Shafa a Najeriya
Wani Yanki da Ambaliyar Ruwa ta Shafa a Najeriya
Talla

Shugaban Kungiyar Agaji ta Red Cross a Jihar Plateau Manasie Phampe yace sun zakulo gawawwakin mutane 40 da ruwa ya tafi da su.

A cewar Mista Phampe an samu ambaliyar ne sakamakon ruwan sama da aka tabka da ya yi sanadiyar ballewar Dam din Lamingo da ke makwabtaka da birnin Jos.

A ranar Lahadi ne da misalin karfe 9:00 na safe aka fara ruwan sama lokacin da mafi yawanci mutane sun shige gidajensu.

Cikin wadanda suka rasa ‘Yan uwansu, har da Abdulhamid Useni, wanda yace yaransa bakwai sun mutu.

Yanzu haka kungiyar agajin gaggawa ta NEMA tace tana ci gaba da binciken gawawwaki tare da taimakon ‘Yan Sanda.

A makon jiya an samu ambaliyar ruwa a Najeriya a biranen Lagos da Ibadan shiyar kudu masu Yammaci inda mutane uku suka mutu bayan samun mutuwar wasu mutane 102 a bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.