Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun harbe wani Dan majalisar Jaha a Arewacin Najeriya

Wasu ‘Yan bindiga sun harbe wani Dan majalisar Jaha, a garin potiskum cikin Jahar Yobe da ke Arewacin Najeriya.  

Gwamnan Jahar Yobe, Ibrahim Geidam
Gwamnan Jahar Yobe, Ibrahim Geidam Leadership Newspaper
Talla

‘Yan sandar Jahar sun bayyana cewa ‘Yan bindigar sun harbe Dan majalisar mai suna Adamu Deguri, a kofar gidansa da ke Unguwar Tandari a birnin Potiskum.

Bayanan da ‘Yan sandar su ka bayar, ya nuna cewa ‘Yan bindigar sun kai harin kan Dan majalisar ne a ciki wata mota kirar Bas, wacce ba ta lamba bayan sun bi shi a baya inda su ka bindige shi a yayin da ya ke kokarin fitowa a motarsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.