Isa ga babban shafi
Najeriya

Matsalar Injin ce sanadiyar hadarin jirgin Dana a Najeriya

Hukumar kula da sufurin jiragen Sama a Najeriya tace matsalar Injin ya janyo hadarin jirigin kamfanin Dana da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 153 a birnin Legas. Rahotanni daga Najeriya sun ce akwai mutane sama da 160 da hadarin jirigin ya rutsa da su a gidajensu.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da gwamnan Legas a lokacin da suke kai ziyara inda jirgin Dana ya yi hadari
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da gwamnan Legas a lokacin da suke kai ziyara inda jirgin Dana ya yi hadari Reuters / Akintunde Akinleye
Talla

Har yanzu dai babu sahihin bayani game da dalilin da suka yi sanadiyar hadarin jirgin Dana mai Lamba MD83 wanda ke shirin sauka a filin jirgin Murtala Muhammad a Legas daga hanyarsa zuwa Abuja.

Amma shugaban hukumar kula da Sufurin Jiragen sama a Najeriya, Mista Harold Demuren yace jirgin ya yi hadari ne bayan Injinan jirgin guda biyu sun dai na aiki.

Rahotanni Daga Lagos sun ce an samu nasara zakulo gawawwaki sama da 140 a wajen da jirgin ya yi hadari.

Masu aikin agaji sun ce, suna saran samun wasu gawawwaki mutanen da jirgin ya fada akan gidajensu.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda ya kai ziyara wajen da aka yi hadarin, ya yi alkawalin inganta sufurin jiragen sama a kasar.

An bayyana hadarin Jirgin Dana a matsayin hadari mafi muni da aka samu a Najeriya tun shekarar 1992 a lokacin da wani Jirgi ya yi hadari inda ya kashe mutane 200 a birnin Lagos.

Yanzu haka hukumar kula da Sufurin Jirage ta kaddamar da binciken gano musabbabin hadarin tare da hadin gwiwar hukumar kiyaye hadurran sufuri ta Amurka.

Gwamnatin China tace akwai ‘Yan kasarta guda Shida da hadarin jirgin ya rutsa da su.

Gwamnatin Faransa tace akwai wata mace Bafaranshiya da hadarin jirgin ya rutsa da ita.

Tuni Amurka ta aiko da Sakon Ta’aziya ga Gwamnatin Najeriya bisa hasarar rayukan da aka samu sanadiyar Hadarin jirgin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.