Isa ga babban shafi
Sharhin Jaridu

Sharhin Jaridun Afrika: 4 ga watan Yuni 2012

Labarin hadarin jirigin Dana a Najeriya shi ne ya mamaye yawancin Jaridun Afrika wanda ya yi sanadiyar mutuwar Fasinjojin jirigin 153.

Jaridun Afrika a cikin Taswirar Afrika
Jaridun Afrika a cikin Taswirar Afrika
Talla

Jaridar Guardian a Najeriya ta buga babban Labarinta mai taken “Tafiyar mutuwa”. Jaridar The Punch ta buga Labari game da al’amarin mai taken ‘Bakar ranar Lahadi! Mutane 153 sun mutu a hadarin jirgi a Legas. Yawancin Jaridun Najeriya sun ce akwai manyan Mutane da hadarin ya rutsa da su wasunsu malaman Jami’a da ma’akatan kamfanin Mai na NNPC.

A wasu labaran Jaridun Afrika, Jaridar Daily Nation ta kasar Kenya ta buga labari mai dauke da tambayar “ Ko za’a samu Fafaroma a Afrika”

Jaridar ta yi hasashen wanda zai gaji Fafaroma Jonh Paul na Biyu inda jaridar tace babu wanda ya cancanci mukamin sai dan Najeriya Malamin Catolika Francis Arinze.

Jaridar Daily Monito ta kasar Uganda ta buga wani labari da ke bayani game da bukin juyayin mutuwar wasu mutane 22 da aka kone karkashin umurnin Kabaka Mwanga na Biyu, Sarkin Buganda saboda sun bijerewa kiran sauya addininsu.

Jaridar tace an gudanar da bukin ne cikin tsauraran matakan tsaro.

Jaridar tace a lokacin da yake Jawabi, Mataimakin shugaban kasa, Ssekandi ya yi kira ga malaman addini yin wa’azi da zai wayar da kan jama’a game da ci gaban tattalin arzikin kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.