Isa ga babban shafi
Algeria

Ana zaman makoki a Algeria bayan mutuwar shugaban kasar na Farko

Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Boutflika ya ware kwanki biyar biyar domin juyayin mutuwar shugaban Algeria na farko Ahmed Ben Bella wanda ya mutu yana da shekaru 96.

Shugaban kasar Algeria na Farko Ahmed Ben Bella
Shugaban kasar Algeria na Farko Ahmed Ben Bella © AFP
Talla

Ben Bella wanda tsohon Sojan Faransa ne a zamanin mulkin Mallaka, yana cikin wadanda suka yi gwagwarmayar samun ‘Yancin kai a Algeria.

Ben Bella shi ne ya samar da wata kungiya domin yakin neman ‘Yanci, kuma Kungiyar ce ta rikide ta zama jam’iyyar Siyasa mai mulki ta FLN.

A shekarar 1963 ne aka zabi Ben Bella a matsayin shugaban kasa, kafin shekarar 1965 da Sojoji suka hambarar da gwamnatinsa tare da kargame shi a cikin gida na tsawon shekaru 15.

Daga baya ne Ben Bella ya samu mafaka a kasar Switzerland inda ya kwashe shekaru kafin ya dawo Algeria a shekarar 1990.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.