Isa ga babban shafi
Najeriya

Wamakko ya lashe zaben Sakkwato amma ‘Yan adawa sun ce magudi aka tabka

Jam’iyyun adawa a Jahar Sakkwato sun kalubalanci sakamakon zaben da aka bayyana Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya lashe inda suka yi zargin tabka magudi tare da gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da zaben Gwamnan wa’adi na biyu.

Alh. Aliyu Magatakarda Wamakko Gwamnan Jahar Sakkwato tare da mataimakinsa Muntari Shagari
Alh. Aliyu Magatakarda Wamakko Gwamnan Jahar Sakkwato tare da mataimakinsa Muntari Shagari NAN/Nigeria
Talla

Zuwa karshen mako ne ake sa ran sake rantsar da Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko karo na biyu a matsayin Gwamnan Jahar Sakkwato bayan da hukumar zabe ta bayyana cewa shi ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar Assabar.

02:05

Rehoton Faruk Muhammad Yabo

Faruk Yabo

A makon jiya ne kotun kolin Najeriya ta tumbuke Wamakko daga fadar gwamnatin Sakkwato, sai dai bayan gudanar da zaben zai sake karbar rantsuwar shugabancin Sakkwatawa bayan fara karbar rantsuwar a shekarar 2007.

A shekarar 2008 ne aka fara soke zaben shi amma daga baya aka sake gudanar da zabe inda ya karbi rantsuwa ta biyu. A watan jiya ne kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa wa’adin Mulkin Wamakko ya kawo karshe tare da sauran gwamnoni Jahohi guda hudu wanda hakan ne ya haifar da sake gudanar da zabe a ranar Assabar.

Hukumar zabe a Jahar Sakkwato tace Wamakko ne ya lashe zaben a kananan hukumomi 23 karkashin Tutar Jam’iyyar PDP da rinjayen kuri’u 518,247. Abokin hamayyarsa ne Yusha’u Ahmed Mohammed na Jam’iyyar ANPP ya zo a matsayi na biyu da yawan kuri’u 131,048.

Sai dai Jam’iyyun adawa sun ce basu yarda da sakamakon zaben ba domin sun ce an yi magudi a zaben kuma magoya bayan Jam’iyyar ANPP sun gudanar da zanga-zanga domin kalubalantar zaben gwamnan da aka bayyana Wamakko ne ya lashe zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.