Kwararru daga Turai na Duba Zaben Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Kwararru daga kasashen Turai na kasar janhuriyar Democradiyya ta Congo domin duba yiwuwar gyara game da zaben kasar na watan Nowamba na shekarar data gabata ta 2011.
Wallafawa ranar:
Kwararrun daga cibiyar Bincike na Democradiyya, da Cibiyar lura da Harkan zabe dake Amurka, tun jiya suka isa kasar inda zasu gana da kungiyoyi da dama.
Sakamakon zaben dai wanda ya baiwa Shugaba Joseph Kabila karin wa'adin zarcewa da mulkin na tsawon shekaru biyar, ya haifar da rudanin gaske cikin kasar, saboda zargin an tafka magudi, musamman daga shugaban 'yan adawan kasar Etienne Tshisekedi, wanda ya yi gaban kansa, ya rantsar da kansa a matsyain Shugaban kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu