Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Jam’iyyar Ouattara ta lashe zaben ‘Yan Majalisa

Jam’iyya mai mulki a kasar Cote d’Ivoire ta shugaba Alassane Ouattara ta samu rinjayen kujeru kashi 80 a zaben ‘Yan Majalisu da aka gudanar a kasar, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar a yau Juma’a .

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan bayyana sakamakon zaben 'Yan Majalisu
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan bayyana sakamakon zaben 'Yan Majalisu REUTERS/ Thierry Gouegnon
Talla

Sai dai Jam’iyyar Tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo ta kauracewa zaben.

A cewar Youssouf Bakayoko shugaban hukumar zaben kasar, Jam’iyyar Ouattara ta RDR ta lashe kujeru 127 cikin 254, inda Jam’iyyar PDCI ta samu kujeru 77

Mista Bakayoko yace kashi 36.56 ne suka kada kuri’a a zaben fiye da zaben da aka gudanar a shekarar 2000 amma kasa da zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamba inda aka samu kashi 80 na masu kada kuri’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.