Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

An yi zaben Cote d’Ivoire cikin lumana amma Jam’iyyar Gbagbo ta kaurace

Al’ummar Kasar Cote d’Ivoire, na dakun sakamakon zaben ‘Yan Majalisun da aka gudanar a jiya Lahadi, wanda ake saran Jam’iyyar Shugaba Alassane Ouattara zata samu gagarumin rinjaye bayan da ‘Yan adawa suka kauracewa zaben.

Wata Mata da goyo zata kada kuri'arta a zaben 'Yan Majalisu a kasar cote d'Ivoire
Wata Mata da goyo zata kada kuri'arta a zaben 'Yan Majalisu a kasar cote d'Ivoire RFI
Talla

Jami’an gudanar da zaben sun ce a gobe talata ne ake saran bayyana sakamakon zaben.

A cewar Bert Koenders wakilin Majalisar Dunkin Duniya, an gudanar da zaben cikin kwaciyar hankali da lumana a ziyarar da suka kai a wasu mazabu a birnin Abidjan.

Sai dai Jam’iyyar tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo ta kauracewa zaben wanda yanzu haka yana birnin Hague bisa zarginsa da aikata laifukan yaki da cin zarafin Bil’adama da magoya bayansa suka yi.

Masu sa ido a zaben sun ce an samu rashin fitowar masu kada kuri’a a zaben sabanin kashi 70 da suka fito jefa kuri’a zaben shugaban kasa da aka gudanar a bara tsakanin Gbagbo da Ouattara.

Sama da mutane Miliyan 5 ne ke da ‘yancin kada kuri’a a zaben ‘yan majalisu da ke da matukuar muhimmaci ga ci gaban siyasar kasar bayan kwashe shekaru ana tabka rikici a cikin kasar.

Sama da ‘Yan takara 1,000 ne suka shiga zaben domin neman kujeru 255.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.