Isa ga babban shafi
NATO-Libya

NATO zata kawo karshen yakinta a Libya

A yau litinin ne kungiyar NATO zata kawo karshen yakinta a kasar Libya a dai dai karfe 11:59 na dare bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dunkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da janye dakarun da suka kwashe watanni bakwai suna luguden wuta ta amfani da jirage sama.Yanzu haka jiragen yakin NATO sun dai na shawagi a sararin samaniya bayan harba bama bamai sama da 6,000 da suka taimaka wa ‘yan tawaye kawo karshen Kanal Gaddafi.An yanke hukuncin ficewar NATO ne duk da kiran da sabuwar gwamnatin Libya ke yi na tsawaita zaman NATO cikin kasar har zuwa karshen shekara domin kaucewa barazana daga dakarun Marigayi Kanal Gaddafi.Sai dai Kungiyar NATO tace rayuwar fararen hula a Libya bata cikin wata barazana bayan da sabuwar gwamnati ta bayyana samar da ‘yancin Libya sanadiyar karbe ikon birnin Sirte da kashe Kanal Gaddafi.Yanzu haka kuma kasashen Turai kawayen Libya suna neman hanyoyin da zasu bi wajen kokarin gina sabuwar gwamnatin Libya.Tun da farko kasashen Rasha da China da Brazil da Africa ta Kudu sun soki wannan matakin na Majalisar Dunkin Duniya inda suka zargi NATO da wuce gona da iri..  

Sakatare Janar na Kungiyar NATO/ OTAN, Anders Fogh Rasmussen, lokacin da yake jawabi akan nasarar yakinsu a Líbia.
Sakatare Janar na Kungiyar NATO/ OTAN, Anders Fogh Rasmussen, lokacin da yake jawabi akan nasarar yakinsu a Líbia. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.