Isa ga babban shafi
Libya

Gwamnatin rikon kwarya ta tabbatar da ‘Yancin Libya

Gwamnatin Rikon kwaryar Libya, ta sanar da Yantar da kasar daga mulkin kama karya, a wani gagarumin buki da aka gudanar a Benghazi, wanda ya samu halartar daruruwan mutane.Jagoran Gwamnatin, Mustafa Abdul Jalil, ya yaba da duk wadanda suka bada gudummawa wajen samun nasarar kawo karshen mulkin shekaru 40 na Kanal Muammar Ghaddafi.Al ‘ummar Libya da kasashen duniya suna fatar ganin kasar ta cim ma gurinta na kokarin girka Mulkin demokradiyya kamar kasar Tunisiya da ta jagoranci Zanga-zanga bayan hambarar Zine Al-Abidine Ben Ali.Wasu Al’umma musulmi a kasar sun fara kokawa dangane da rashin aiwatar da jana’izar Gaddafi cikin lokaci kamar yadda Addinin Islama ya tanadar.A Jawabin Jalil Jagoran gwamnatin ‘Yan Tawaye, yace zasu tabbtar da mulkin Shari’a kamar yadda suka yi alkawali tun fara boren adawa da Gaddafi.Wannan Sanarwar ta samun ‘yancin Libya zata kasance tafarkin samar da wata sabuwar gwamnati da sabon kundin tsarin mulki da zai tabbatar Demokradiyya a shekarar 2013. 

Daruruwan mutane dauke da tutar Libya a bukin tabbatar da 'yancin Libya
Daruruwan mutane dauke da tutar Libya a bukin tabbatar da 'yancin Libya REUTERS/Suhaib Salem
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.