Isa ga babban shafi
Libya

UN ta yi gargadi kan yunkurin kisan Gaddafi

Hukumar kare hakkin Bil adama ta Majalisar Dunkin Duniya ta gargadi ‘yan Tawayen Libya dake farautar shugaba Gaddafi don neman kashe shi.A cewar hukumar babu dokar da ta amince da matakin kisa ba tare da kotu ta yanke wa mutun hukunci ba.A cewar Kakakin hukumar Rupert Colville bin doka da Oda na da muhimmacin gaske, kuma wannan ya shafi Gaddafi da kowa da kowa.A ranar laraba ne dai ‘Yan Tawayen Libya suka bada sanarwar bada kyautar kudi kimanin kudin Amurka Dala Miliyan 1.67 ga duka wanda ya kawo Gaddafi a mace ko a raye.A wannan yunkurin ne shugaban ‘Yan Tawayen na Libya Mustapha Abdel Jalil ya yi tayin Afuwa ga duk mambobin Gaddafi masu masa biyayya idan har suka cafko shi a raye ko suka kashe shi.Sai dai kuma Mista Colville yace matakin cafko Gaddafi a raye ita ce hanya madaidaiciya wanda hakan zai bada damar gurfanar da shi a gaban babban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.