Isa ga babban shafi
Zambia

Tsohon Shugaban Zambiya Chiluba ya bar duniya ya na da shekaru 68

Tsohon Shugaban kasar Zambiya Fredrick Chiluba wanda ya kawo karshen mulkin jam’iyya daya, ba a bayyana sanadiyar mutuwar ba, amma ya yi  fama da chutuka masu nasaba da zuciya da koda.Dan shekaru 68 da haihuwa, ya cika a gidansa dake Lusaka babban birnin kasar da sanyin safiyar yau Asabar, kafin akai gawar wajen adanawa a asibiti.Cikin shekarar 1991 Chiluba, ya karbi madafun ikon kasar ta Zambiya dake yankin Kudancin Afrika, inda ya mulki kasar na shekaru 10, wato 1991 zuwa 2001.Shi ne ya kawo karshen mulkin shekaru 27 ha Shugaban kasar na farko Kenneth Kaunda. Daga bisani Marigayi Fredrick Chiluba ya fuskanci zargin cin hanci na rasha, amma kotu ta wanke shi bayan sharia na shekaru shida. 

Tsohon Shugaba Marigayi Frederick Chiluba na Zambiya
Tsohon Shugaba Marigayi Frederick Chiluba na Zambiya AFP PHOTO / THOMAS NSAMA
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.