Isa ga babban shafi
Libya

Manyan kasashe zasu tallafa wa 'yan tawayen Libya da kudade

Yanzu haka dai masu biyar diddigin yakin basasar da ake tabkawa a kasar Libiya, sun fara lissafawa shugaban kasar Ma’amar Kaddafi kwanakin da suka rage masa kan karagar shugabancin kasar, ganin irin yadda dakarun tsaron NATO ko OTAN ke ci gaba da karya lagon karfin sojan da ya ke da shi.Wannan daidai lokacin da manyan kasashe ke neman tallafawa 'yan tawayen da kudade. Tuni Shugaban kasar Senegal Abdullahi Wade, ya nemi taikawa shugaba Muammar Gaddafi ya ajiye mulkin kasar ta Libya cikin tsakani.A jiya ne shugaban kasar Senegal Abdullahi Wade, ya ziyarci birnin Benghazi dake rike ga hannun 'yan tawayen kasar ta Libiya.Anata bangaren Kungiyar Tsaron Tekun Arewacin Atlantika NATO ko OTAN ta ce wannan aiki na kare fararen huar Libya da ta fara sai ta kammala. Domin kare hare hare shugaba Gaddafi kan yunkunan da suka yi masa bore.

(REUTERS)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.