Isa ga babban shafi
Libya

An ci gaba da fada a garin Misrata na Libya bayan sanarwar tsagaita wuta

An ci gaba da jin karar manyan makamai da safiyar yau Lahadi, a garin Misrata na kasar Libya, abunda musanta ikirarin gwamnatin kasar na tsagaita wuta.Tunda fari Mataimakin Ministan harkokin wajen kasar Khaled Kaim ya bayyana cewa sojojin kasar sun tsagaita wuta na kai hare hare garin Misrata, domin shugabannin kabilu zasu taimaka wajen warware matsalar. Wannan daidai lokacin da kasar Amurka ta fara amfani da jiragen saman da babu matuki wajen kai hari, domin tabbatar da kudirin MDD da ya haramta shawagin jiragen sama da kuma kare fararen hula.Kafin wannan ikirari na tsagaita wuta daga gwamnatin kasar ta Libya, an hallaka akalla mutane 24, yayin da dakarun gwamnati suka yi wa garin kawanya, na neman karbewa.Kungiyoyin kare hakkin bil Adam sun bayyana mutuwan mutane 1000 cikin makonni da aka wakshe ana dauki ba dadi a birnin. 

REUTERS/Yannis Behrakis
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.