Isa ga babban shafi
Africa ta kudu

Shugaban Afrika ta Kudu Zuma zai gana dana Libya Gaddafi

Rohotanni daga kasar Afrika ta kudu, sun ce shugaba Jacob Zuma, zai je kasar Libya makon gobe, dan tattauna yadda shugaba Mummar Ghadafi zai bar karagar mulki, yayin da kungiyar kawancen NATO ko OTAN ke ci gaba da kai hare hare kan Tripoli babban birnin kasar.Ranar Litinin ake saran Zuma zai kai ziyarar, kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta Afrika ta Kudu ta bayyana. Manyan kasashen duniya, sun kekashe kasa sai sun raba Gaddafi da karagar mulki, yayin da shugaban ke cewa ba zai sauka ba, bayan mulkin shekaru 42. 

Shugaban Libya Muammar Gaddafi dana Afrika ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban Libya Muammar Gaddafi dana Afrika ta Kudu Jacob Zuma ®Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.