Isa ga babban shafi
Tunisiya

Kasashen Tunisiya da Faransa sun amince da hadakar soja

Gwamnatin kasar Tunisiya da kasar Fransa sun saka hannu kan wata yarjejeniyar huldar samar da cibiyar horar da aiyukan soja a yankin Gafsa dake kudancin kasar, wanda zai lashe kimanin miliyan 3, da dubu 100 na Euro, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Tap ya ruwaito.A dai bangaren kuma gwamnatin kasar ta Tunisiya ta bayyana aniyarta na shigar da karar kasar Libiya a gaban MDD, bayan da sabin makaman rokokin kasar Libiya suka fada a cikin kasarta, a yankin kan iyakar Dehiba dake kudancin kasar. 

REUTERS/Zoubier Souissi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.