Isa ga babban shafi
Tunisiya

A Tunisiya Kotu Ta Daure 'Yan Al-Qaeda Bakwai

Wata kotu a kasar Tunisiya ta daure wasu mutane bakwai  saboda zarginsu da zama ‘yan kungiyar Al-Qaeda.Biyu daga cikin su, Hichem Ben Rabeh da Samir Dridi wadanda zasu zauna gidan yari na tsawon shekaru bakwai.Wasu murtun biyu za'a daure su ne na tsawon shekaru biyar yayin da saura mutane uku aka daure su na tsawon shekara daya kowanne.Lauyan su Samir Ben Amor yace dukkaninsu shekarun su tsakanin 23 zuwa 28 ne.Ana zargin su da laifin kulle-kullen tafiya kasar Algeria domin taimakawa wasu ‘yan kungiyar Al-Qaeda. 

Tutar kasar Tunisiya
Tutar kasar Tunisiya RFI Hausa
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.