Isa ga babban shafi
Libya

Kasashen Duniya zasu tallafawa ‘Yan tawayen Libya

A kokarin neman ganin shugaban Libya Muammar Gaddafi ya bar karagar mulki, A wata Hadin gwiwar wasu kasashen yammaci da kasashen larabawa, kasashen sun amince su tallafawa ‘Yan tawayen libya da Miliyoyin Daloli domin cim ma gurinsu na kawar da shugaban.A jiya Alhamis ne a Birnin Rom na Itali Ministocin kasashen da ke adawa da Gwamnatin ta Gaddafi suka amince da wannan matakin, wadanda suka hada da kasar Amurka da Faransa da Kasar Birtaniya da Itali da Qatar da Kuwait da kuma kasar Jordan.Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Cilinton tace Amurka zata sauya al’amurra domin samar da dokar da zata bada damar tallafawa ‘yan Tawayen daga cikin asusun kudaden kasar ta Libya da aka rufe a kasar Amurka.Sai dai mataimakin ministan harakokin wajen Libya Khaled Kaim ya la’anci wannan matakin na amfani da kudaden asusun bankunan kasar da aka rufe domin tallafawa ‘yan tawayen da ke adawa da Gwamnatin Muammar Gaddafi.A yanzu haka dai kasar Kuwait tace zata ware kudi dalar Amurka Miliyan 180, kamar yadda kasar Qatar ita ma ta bayyana cewa zata ware kudi dala Miliyan 400. 

Wakilan kasashen da suka amince da tallafawa 'yan tawayen kasar Libya
Wakilan kasashen da suka amince da tallafawa 'yan tawayen kasar Libya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.