Isa ga babban shafi
Libya

Dakarun Shugaban Libya Gaddafi na ci gaba da kai hare hare

Dakarun Shugaba kasar Libya, Muammar Gaddafi, na ci gaba da kai hare hare garuruwan Adjadabiya da Misrata, abin da ya tilastawa daruruwan mutane gujewa gidajensu.Prime Ministan Birtaniya, David Cameron, ya ce babu wani shiri na tura dakarun kasa, cikin kasar ta Libya. Amma za a ci gaba da aikin tabbatar da kudirin MDD da ya haramta shawagin jiragen sama da kare fararen hula.Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akalla bakin haure 12,000 suka isa Tunisiya, daga kasar Libya, saboda ci gaba da tashin hankalin da akeyi a cikin kasar.Mai Magana da yawun Hukumar, Andrej Mahecic, ya ce tsakanin asabar da jiya Lahadi, bakin haure 5,000 suka tsallaka kasar. 

Reuters/Zohra Bensemra
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.