Isa ga babban shafi
Tunisia

An dakatar da Jam’iyyar Ben Ali a Tunisiya

Ministan kula da harakokin cikin gidan Tunisiya ya sanar da dakatar da jam’iyyar tsohon shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali, Fahrat Rajhi ya bayyana cewa dukkanin taruka da gamgamin Jam’iyyar an haramta gudanar da su tare da rufe dukkanin ofishin Jam’iyyar a kasar.Wannan sanarwar dai na zuwa ne bayan wani sabon rikicin da ya balle a kudancin kasar wanda ya yi sanadiyar mutuwar saurayi daya, Kuma ya mutu ne bayan shakar hayaki mai sa hawaye a lokacin bata kashi tsakanin jami’an tsaron kasar da masu zanga-zanga a birnin Kebili dake yankin kudancin kasar.An dai ta samu barkewar rikici a Gafsa inda masu zanga-zanga ke neman ganin an tsige shugaban ‘yan sandan kasar Khaled Ghazouani daga mukaminsa. Wannan yankin ne dai masu zanga-zanga suke neman tilastawa Gwamnan yankin yayi murabus.A makon daya gabata ne gwamnatin rikon kwaryar kasar ta sauya shugabanin ‘yan sandan da Gwamnoni na yankunan kasar 24 domin kwantar da zanga-zangar da ke ci gaba da gudana a kasar. 

hambararren shugaban kasar Tunisia Ben Ali
hambararren shugaban kasar Tunisia Ben Ali Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.