Isa ga babban shafi
Nijar

Na hannun damar Tandja ya kai ga zagaye na biyu a zaben Nijar

Sakamakon zaben kasar Jamhuriyyar Nijar a zagayen farko na nuna cewa na hannun damar tsohon hambararren shugaban kasa Mamadou Tandja ya samu nasarar kai wa zagaye na biyu a zaben da zai samar da zababben shugaban kasa wanda kuma zai kawo karshen mulkin soji a kasar.Tsohon Prime ministan kasar Seyni Oumarou na Jam’iyyar MNSD nasara kuma na hannun damar tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja shi ne yazo na biyu a zagayen farko na zaben da kuri’u kashi 43, sai Mahamadou Issoufou na Jam’iyyar PNDS Tarayya shi ne yazo na Farko a zaben.Sai dai kuma ana hasashen cewa Oumarou na Jamiyyar MNSD Nasara kan iya lashe zaben ganin kawancen da jam’iyyarsa ta shiga da jam’iyyun kasar kusan Ashirin wadanda suka amince su kulla kawancen, sati daya da fara gudanar da zaben zagayen farko.Kodayake wannan kawancen na hadakar Jam’iyyun kasar ya janyo kace-na ce tsakanin abokan hamayyar jam’iyyar MNSD, wadanda suke ganin Jam’iyyar ba abun yarda bace da za’a daurawa amanar shugabanci tun bayan da Jam’iyyar ta taimakawa tsohon shugaba Tandja sauya kundin tsarin mulkin kasar don bashi damar yin tazarce wanda hakan ne kuma ya janyo sojoji a kasar suka kwace mulkin daga hannun farar hula.Shugaban mulkin sojin kasar salou Djibo wanda ya hambarar da gwamnatin Tandja a watan Febrairun shekarar bara, ya jandada alkalinsa na barin madafan iko a watan Aprilun shekarar nan. 

Seini Oumarou Na jam'iyyar MNSD Nasara a Jamhuriyyar Nijar.
Seini Oumarou Na jam'iyyar MNSD Nasara a Jamhuriyyar Nijar. AFP/PIUS UTOMI EKPE
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.